Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta umarci a gudanar da bincike kan wasu jami’anta da aka gani a wani bidiyo suna jan ɗan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, bayan zaman kotu a Abuja.
Matakin ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar na tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari ƙarar da ya shigar kan batun belinsa. Alƙali Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne bayan ya yi watsi da buƙatar Sowore na janyewar alƙalin daga shari’ar bisa zargin nuna son kai.
A wata sanarwa, mai magana da yawun DSS, Favour Dozie, ya ce shugaban hukumar ya bayar da umarnin gaggauta bincike kan yadda jami’an suka gudanar da lamarin. Ya kuma bayyana cewa Sowore ne ya zaɓi shiga motar DSS maimakon ta hukumar gidajen gyaran hali.
DSS na tuhumar Sowore ne kan wasu kalamai da ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ake zarginsa da kiran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da “mai laifi”. Hukumar ta ce tun a shekarar 2025 ta nemi ya janye kalaman kafin daga bisani ta garzaya kotu domin neman fassarar doka kan irin waɗannan kalamai da ake yi game da shugaban ƙasa.