Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya janye shirinsa na sayen ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke buga gasar Firimiya ta Ingila, saboda yana buƙatar kuɗin domin kammala aikin matatar mai tasa da ta kai darajar dala biliyan 20 a Legas.
Hamshaƙin attajirin ya bayyana hakan ne a wata hira ta podcast da Nicolai Tangen, Babban Daraktan Hukumar Zuba Jari ta Norges Bank Investment Management, wadda aka fitar a ranar Laraba ta shafin YouTube na hukuma na kamfanin.
Dangote, wanda shi ne wanda ya kafa kuma Babban Daraktan Kamfanin Dangote Group, ya ce a lokacin da yake tunanin sayen Arsenal da gaske, darajar ƙungiyar ta kai kusan dala biliyan 2, amma ya yanke shawarar karkatar da kuɗin zuwa harkokin kasuwancinsa.
Ya ce:
“A lokacin da na mayar da hankali sosai wajen sayen Arsenal, a lokaci guda kuma ina fuskantar ƙalubalen tabbatar da an kammala matatar mai, takin zamani, da kuma masana’antar sinadarai.”