Ministan kudi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Najeriya ke aiwatarwa sun zama shaida ga kasashen Afirka cewa daukar matakai masu karfi da aiwatar da tsare-tsare yadda ya kamata na kawo ci gaba.

Oyedele ya ce Najeriya ta nuna cewa lokaci ya yi da za a daina yawan maganganu kawai, a mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki domin samun ingantaccen ci gaba da habaka tattalin arzikin kasa.

Ya kara da cewa sauye-sauyen da ake yi na taimakawa wajen karfafa tattalin arziki da kuma bude sabbin damammaki ga masu zuba jari da ‘yan kasuwa.