Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da gwamnatinsa ta dauka na tallafawa matatar Dangote, yana mai cewa da ba a samu karfin tace mai a cikin gida ba, da Najeriya ta shiga cikin babbar matsala sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a duniya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin taron Africa CEO Forum karo na 13 da aka gudanar a kasar Rwanda.
Shugaban kasar ya ce yawan al’ummar Najeriya da kuma dogaro da kayayyakin man fetur ya sa ya zama wajibi gwamnati ta mara baya ga ayyukan tace mai na cikin gida kamar matatar Dangote.
“Duba da rikice-rikicen da ke faruwa a sassan duniya, Najeriya mai mutane sama da miliyan 200 ba za ta iya rayuwa ba tare da matatar mai ba,” in ji Tinubu.