Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga mambobi da masu neman takara da shugabannin jam’iyyar APC da su nuna dattako yayin gudanar da zabukan fidda gwani a fadin kasar nan.

Tinubu ya gargadi cewa duk wani rikici ko rashin jituwa zai amfani ne kawai ga jam’iyyun adawa, sannan ya shawarci wadanda suka yi nasara da kada su yi alfahari fiye da kima, yayin da ya bukaci wadanda suka fadi zabe su karbi sakamakon cikin mutunci.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, gabanin fara zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar wakilai, Tinubu ya bayyana cewa zabukan ba wai kawai domin zakulo ‘yan takarar jam’iyya ba ne, har ila yau wata hanya ce ta gwada hadin kai, juriya da karfin jam’iyyar APC yayin da take tunkarar zagayen zabuka karo na hudu.

Ya ce, “A kowace gasa dole akwai mai nasara da wanda bai yi nasara ba. Ina kira ga wadanda suka yi nasara da kada su raina wasu saboda nasarar da suka samu, yayin da nake rokon wadanda suka fadi zabe su nuna dattako tare da shirya wata dama a gaba