Hukumar Yaƙi da Rashin Ilimin Bai Daya ta Kasa (NMEC) ta bayyana cewa matsalolin rashin tsaro, talauci da kuma auren wuri na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa karuwar matasan da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Hukumar ta ce yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da rikice-rikice a wasu sassan kasar nan na tilasta wa iyalai da dama kauracewa makarantu, yayin da matsin tattalin arziki ke hana wasu iyaye iya daukar nauyin karatun ‘ya’yansu.
NMEC ta kuma nuna cewa auren wuri, musamman a wasu yankuna, na ci gaba da hana yara mata samun damar ci gaba da karatu.
Hukumar ta jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, al’umma da masu ruwa da tsaki domin magance matsalar tare da tabbatar da cewa yara da matasa sun samu damar ilimi