Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce kamfaninsa ya yi watsi da buƙatar da kamfanin mai na Najeriya NNPC ya gabatar ta neman ƙara yawan hannun jarinsa a matatar man Dangote da kashi 7.25 cikin 100.
Dangote ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da shugaban asusun zuba jari na Norway, Nicolai Tangen.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an samu ƙaruwar man da ake tacewa a matatar mai da ke Lekki zuwa lita biliyan 3.18 a watanni uku na farkon 2026 yayin da man da ake shigowa da shi ya ragu sosai da lita miliyan 965.52.
Binciken da aka ƙara yi ya nuna cewa yaƙin Amurka da Iran da ya janyo matsalar mai ya haifar da ƙaruwar kuɗin shiga ga matatar Dangote yayin da matatar ta ƙara yawan tataccen man da take fitarwa.
A cewar Dangote a hirar da ya yi, an ƙi amincewa da tayin NNPC na ƙara kashi 7.25 na hannun jarinta a matatar saboda kamfanin yana shirin bai wa sauran ƴan Najeriya damar zuba hannun jarinsu a kamfanin