Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana shirin ta na gudanar da auren gata karo na uku, inda za ta aurar da zawarawa 300 domin tallafa wa mata da kuma inganta rayuwar iyalai a fadin jihar.
Kwamishinar Mata da Ci-gaban Yara ta jihar, Hajiya Halima Hassan Kamba, ce ta bayyana hakan yayin da take gabatar da bayanin ayyukan ma’aikatar ta ga manema labarai a Birnin Kebbi.
Ta ce za a gudanar da auren ne a watan Yulin wannan shekara, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na rage matsalolin zamantakewa da kuma taimaka wa marasa ƙarfi.
A cewar ta, shirin yana daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi wajen rage ayyukan ɓarna da kuma taimaka wa mata da maza masu ƙaramin ƙarfi da ke son yin aure amma matsin tattalin arziki ya hana su.