Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nada Ibrahim Adam a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai (Special Adviser on Information), a wani yunƙuri na ƙara bai wa matasa damar shiga harkokin mulki tare da inganta isar da ayyukan gwamnati ga al’umma.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ibrahim Adam, mai shekaru 32 a duniya, ya kammala karatun Digiri a fannin Kimiyyar Siyasa (Political Science) daga Jami’ar Bayero Kano (BUK). Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin matasan masu tasiri a kafafen sada zumunta da suka taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa nasarori da ayyukan gwamnatin Kano mai ci.
Kafin wannan naɗin, Ibrahim Adam ya yi aiki a matsayin Mataimaki na Musamman (Personal Assistant) ga Alhaji Abba Kabir Yusuf lokacin da yake ɗan takarar gwamna tsakanin shekarun 2020 zuwa 2022. Daga baya kuma an naɗa shi Mataimaki na Musamman ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso lokacin da yake ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya Ibrahim Adam murnar wannan sabon muƙami tare da ƙarfafa masa gwiwa da ya yi aiki cikin haɗin kai, jajircewa da sadaukarwa wajen isar da sahihan bayanai game da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar Kano ga al’umma.
Majiyar Labari: Nigerian Tracker