Matasan da suka jagoranci zanga-zangar da ta kai ga murabus ɗin Ministan Ilimi na Indiya sun buƙaci gwamnatin ƙasar da ta saki dukkan mutanen da aka kama yayin zanga-zangar da ta gudana na tsawon makonni a sassa daban-daban na ƙasar.

Gangamin, wanda aka yi wa laƙabi da Cockroach Janta Party, ya fara ne saboda zargin kwarmata takardun jarabawa kafin ɗalibai su rubuta su.

A cewar rahotanni, jagororin zanga-zangar sun zargi jami'an tsaro da kama da kuma cin zarafin daruruwan masu zanga-zanga a babban birnin ƙasar da sauran yankuna.

Rahotanni sun kuma nuna cewa har yanzu ana ci gaba da tsare wasu daga cikin waɗanda aka kama a jihohin Assam, West Bengal da Bihar.

Sai dai gwamnatin Indiya ta sanar da amincewa da wasu daga cikin buƙatun masu zanga-zangar, ciki har da sakin dukkan mutanen da aka tsare yayin gudanar da zanga-zangar.