Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Jihar da ta samar da cibiyoyin koyon ƙananan sana’o’i a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin inganta koyon sana’o’i da ƙarfafa matasa su dogara da kansu.
Wannan ya biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ungogo, Sa’ad Aminu Sa’ad, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Litinin.
A cikin ƙudirin, ya buƙaci gwamnati ta kafa cibiyoyin koyon sana’o’i a yankunan Tudun Fulani da Zango da ke ƙaramar hukumar Ungogo.
Sai dai bayan tattaunawar da aka gudanar kan ƙudirin, majalisar ta ga ya dace a faɗaɗa shirin domin ya shafi dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, maimakon takaita shi ga wasu yankuna kaɗai.
A wani ƙudiri daban kuma, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Birni, Nabil Sarki Aliyu Daneji, ya buƙaci gwamnatin jihar ta zamanantar da Asibitin Sabo Bakin Zuwo tare da samar masa da kayan aikin lafiya na zamani.
Ya bayyana cewa asibitin na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Birni da ma sauran mazauna yankunan da ke makwabtaka da ita, don haka ya dace a inganta kayan aikinsa da sauran ababen more rayuwa domin ƙara inganta ayyukan da yake yi.
Majalisar ta tattauna kan ƙudurorin biyu tare da jaddada muhimmancin bunƙasa fannin koyon sana’o’i da kuma inganta harkokin kiwon lafiya a faɗin jihar.