Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation Whirl Stroke sun yi nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai yankin Lande Jessi da ke Ƙaramar Hukumar Lau a Jihar Taraba.
A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, an ƙaddamar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari ƙauyukan Tashan Musa da Barkindan Fulani, inda suka yi garkuwa da mutane biyu tare da kwashe kayan abinci.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Yuli, 2026.
Bayan gudanar da bincike da sintiri a wurare daban-daban, dakarun sun samu nasarar ceto mutanen biyu, waɗanda aka ce sun shafe kusan mako guda a hannun masu garkuwa da mutanen kafin a kuɓutar da su.
Rundunar ta jaddada cewa wannan nasara na nuna ƙudurinta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma, tare da yaƙi da masu aikata laifuka a sassa daban-daban na ƙasar.