Wata kotu a ƙasar Thailand ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa bayan ta same su da laifin kai ɗaya daga cikin munanan hare-haren ta’addanci da aka taɓa gani a ƙasar.

Mutanen biyu, ‘yan ƙabilar Uyghur da ke cikin tsiraru a ƙasar China, an same su da laifin shiryawa da tayar da wani babban bam a ranar 17 ga watan Agustan 2015 a kusa da wani wurin ibada da ke tsakiyar birnin Bangkok, wanda ya shahara ga masu yawon buɗe ido daga ƙasashen waje.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane 20 tare da jikkata sama da 120.

Bam ɗin ya tashi ne kusa da wurin ibadar Erawan, inda ya tarwatsa masu ibada da kuma wasu mahaya babura da ke kusa da wajen, wasu daga cikinsu suka samu mummunan rauni sakamakon gobara.

Rahotanni sun ce harin ya kuma faru kusa da ofishin BBC da ke Bangkok, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a birnin.

An cafke mutanen biyu ne cikin makonni biyu bayan harin, inda aka shafe kusan shekara goma ana shari’a kan lamarin, yayin da dukkanin su suka musanta aikata laifin.

Sai dai an bayyana cewa binciken ‘yan sanda da wasu kura-kurai da aka gano a shari’ar sun haifar da tambayoyi kan sahihancin hukuncin da kotun ta yanke.