Ƙaramin Ministan Tsaro na Najeriya, Bello Matawalle, ya zargi ƴan adawa da ƙoƙarin kambama matsalar tsaro a ƙasar domin ɓata sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Matawalle ya ce ƴan adawa na yaɗa farfaganda ne da nufin karkatar da hankalin jama’a daga abin da ya kira nasarorin da gwamnati ke samu a fannin tsaro da sauran ɓangarori.

Ya bayyana cewa dakarun Najeriya na samun ci gaba mai kyau a yaƙi da ‘yan bindiga, musamman a yankunan arewa maso yammacin ƙasar.

“Babu wata farfaganda ko yaƙin neman siyasa da za ta kauda hankalin shugaban ƙasa daga cika alƙawuran da ya ɗauka wa ‘yan Najeriya,” in ji shi.

Wata sanarwa daga mai taimaka wa ministan kan yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ta ambato Matawalle yana cewa duk da sukar da ake yi, Tinubu na ci gaba da samun goyon baya a sassan arewacin ƙasar.

Ya kuma yi hasashen cewa Shugaba Tinubu zai samu nasara a zaɓen 2027, yana mai cewa jama’a na ganin ci gaban da ake samu musamman a yaƙi da matsalar tsaro.

A cewarsa, ana samun ƙarin ƙaimi a ayyukan soji a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi, wanda ya ce yana haifar da sakamako mai kyau.