An tabbatar da mutuwar ma’aikatan ruwa uku ‘yan ƙasar Indiya bayan wani hari da sojojin Amurka suka kai kan wani jirgin dakon man fetur a mashigin tekun Oman, inda suka zargi jirgin da keta dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa da ke da alaƙa da Iran.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a ranar Laraba kan jirgin MT Settebello, wanda ke ɗauke da ma’aikatan Indiya 24. An ce an ceto mutum 21, yayin da uku suka rasa rayukansu.
Ministan sufurin jiragen ruwa na Indiya, Sarbananda Sonowal, ya wallafa a shafin X cewa ana shirin dawo da gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ƙasar Indiya nan ba da jimawa ba.
Rahotanni sun kuma nuna cewa Amurka ta kai hare-hare kan jiragen ruwa guda uku a cikin tekun Gulf a wannan makon, dukkansu na ɗauke da ma’aikatan Indiya.
A ranar Alhamis, hukumomin Delhi sun ce dukkan ma’aikatan jirgin Jalveer su 20 suna cikin koshin lafiya bayan wani hari da aka kai a Oman.
Haka kuma, kwanaki uku kafin hakan, an ce an ceto ma’aikatan Indiya 24 da ke cikin jirgin Marivex kafin ya nutse.
Cibiyar Kula da Ayyukan Tsaro ta Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da kai farmaki kan jiragen, inda ta bayyana cewa ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ya kai hari ne bayan zargin rashin bin umarni daga ɓangaren ma’aikatan jirgin.