Jagoran jam’iyyar adawa ta NDC a Najeriya, Sanata Seriake Dickson, ya yi kakkausar suka ga wasu magoya bayan Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai zarginsu da ƙoƙarin ɓata sunan jam’iyyar da kuma bijire wa dokokinta.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise, tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya ce NDC ce ta ba Obi da Kwankwaso damar siyasa da dandamalin da suke amfani da shi, ba wai su ne suka yi wa jam’iyyar wata alfarma ba.
Dickson ya bayyana cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen kafuwar jam’iyyar da bunƙasarta tun kafin manyan ‘yan siyasar adawar su shiga cikinta, yana mai nuna rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira ƙoƙarin wasu magoya bayansu na kawo cikas ga tafiyar jam’iyyar.
Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun saɓani tsakanin magoya bayan Obi da Kwankwaso da wasu shugabannin jam’iyyar, musamman bayan rahotannin sauya sunayen wasu ‘yan takara a jihohi daban-daban.
Ya kuma jaddada cewa Obi da Kwankwaso ba su bayar da gudunmawar kuɗi wajen kafa jam’iyyar ba, tare da gargaɗin cewa duk wanda ba zai iya bin dokoki da tsarin jam’iyyar ba, zai iya neman wata hanyar siyasa dabam.