Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa ba ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ba dangane da binciken zargin batar da kuɗaɗe har naira tiriliyan 210.

Lamarin ya biyo bayan muhawarar da ta gudana a wani zaman Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da binciken kuɗaɗen al’umma, wanda ke gudanar da bincike kan yadda aka sarrafa wasu kuɗaɗe a kamfanin.

A cewar rahoton da jaridar The Cable ta wallafa, majalisar ta ce babu wata sanarwa ko matsaya da ta fito daga gare ta da ke nuna amincewa da kama Kyari. Ta kuma yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa bayanan da ka iya haifar da ruɗani, tana mai jaddada cewa binciken zai ci gaba da gudana bisa tanadin doka.

Majalisar ta kuma soki kalaman Sanata Adams Oshiomhole, wanda ya bayyana NNPCL a matsayin “matattarar ɓarayi,” tana mai cewa irin waɗannan kalamai ba sa wakiltar matsayar hukuma.

Haka kuma, kwamitin da ke jagorantar binciken ya ce kalaman Oshiomhole ra’ayinsa ne na kashin kansa, ba matsayar kwamitin ko ta Majalisar Dattawa ba.

A gefe guda kuma, wata sanarwa da aka danganta da Kyari ta nuna rashin jin daɗinsa kan batun kiran a kama shi, tare da bayyana cewa yana ƙasar waje ne domin neman kulawar lafiya.