Aliko Dangote ya bayyana wani gagarumin shiri na samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawat 20,000 domin taimakawa wajen magance matsalar ƙarancin lantarki a Nijeriya.
Sanarwar na zuwa ne a lokacin da Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan jama’a a Afirka, ke ci gaba da fama da matsanancin ƙarancin wuta wanda ke kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziki da ci gaban masana’antu.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da babban daraktan hukumar kula da ‘yan kasuwa a ƙasashe masu tasowa ta International Finance Corporation, Makhtar Diop.
Ya ce rukunin kamfanoninsa zai shiga fannin samar da lantarki domin ƙara tallafawa ci gaban masana’antu da tattalin arzikin Afirka.
“A yanzu za mu shiga fannin lantarki… mu samar da megawat 20,000,” in ji Dangote, yana mai jaddada cewa manyan abubuwan da Afirka ke matuƙar buƙata sun haɗa da makamashi, taki da kuma kayayyakin masana’antu.
Bayan ƙaddamar da katafariyar matatar mai da ke iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 a kowace rana, da kuma samun babban matsayi a kasuwar taki, Dangote ya nuna cewa kamfanoninsa na da isassun kuɗaɗe da kadarori da za su iya taimakawa wajen magance matsalar lantarki a Nijeriya.