Wani harin kwanton ɓauna da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka kai wa dakarun Sojin Najeriya a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna ya yi sanadin mutuwar wani babban jami’in soja tare da wasu sojoji shida.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne yayin da dakarun ke gudanar da sintiri na yau da kullum a yankin, lamarin da ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da jami’an tsaro ke fuskanta wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka a arewa maso yammacin ƙasar.
A cikin ‘yan shekarun nan, hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun ci gaba da addabar al’ummomi da dama a yankin, duk da ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi na murƙushe ayyukansu.
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun sha yin kira ga gwamnati da ta ƙara yawan jami’an tsaro tare da inganta dabarun yaƙi da masu tayar da kayar baya domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.