Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta yi wa jam’iyyar Access Party, wadda aka fi sani da Jam’iyyar Matasa, rajista tare da ba ta damar kammala dukkan matakan da suka rage na rajistar ta.

Jagororin jam’iyyar, Audu Bulama-Bukarti da Mevon Samuel, ne suka shigar da ƙara a kan INEC bayan hukumar ta ƙi amincewa da rajistar jam’iyyar.

INEC ta bayyana cewa ta ƙi amincewa da rajistar ne saboda tambarin jam’iyyar ya yi kama da na wata jam’iyya da aka riga aka yi wa rajista.

Yayin da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Obiora Atuegwu Egwuatu ya ce hukumar ba ta da hurumin hana rajistar jam’iyyar bisa wannan hujja.

Alƙalin ya bayyana cewa matakin da INEC ta ɗauka bai dace da tanade-tanaden doka ba, yana mai cewa ya saɓa da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da kuma Sashe na 79 na Dokar Zaɓe ta 2022.