Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da bibiyar kashe kuɗaɗen al’umma ya buƙaci hukumomin tsaro su kamo tsohon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Mele Kyari, bisa zargin yin kunnen uwar shegu da gayyatar da kwamitin ya yi masa.
Kwamitin ya gayyaci Kyari ne domin ya yi bayani kan wasu tambayoyi da suka shafi binciken kuɗaɗe kusan naira tiriliyan 210, waɗanda kwamitin ya ce har yanzu bai gamsu da bayanin yadda aka sarrafa su ba a lokacin da yake shugabantar kamfanin tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023.
Tun da farko, ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya ne ya fara nuna damuwa kan waɗannan kuɗaɗe, sai dai tsohon babban jami’in kuɗaɗe na NNPCL, Umar Isa, ya musanta zargin ɓacewar su.
A yayin zaman kwamitin, Sanata Victor Umeh ya buƙaci a ɗauki matakin kamo Kyari saboda kin amsa gayyatar majalisar. Nan take mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Peter Nwaebonyi, ya goyi bayan wannan buƙata, yana mai cewa rashin bayyana gaban kwamitin na kawo cikas ga aikinsa.
Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya gargadi cewa Majalisar Dattawa na iya rasa martabarta idan ba ta ɗauki matakin da ya dace wajen tabbatar da bin umarninta ba.