Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kogi ta tabbatar da harin da ‘yan bindiga suka kai a wata makaranta da ke jihar, inda rahotanni suka ce an kashe mataimakin shugaban makaranta, wani dattijo mai shekara 70, da kuma ɗalibi mai shekara shida.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba, ta ce maharan da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki makarantar Government Secondary School da ke garin Iluke Bunu, da nufin kai hari kan ɗaliban da ke rubuta jarabawar WASSCE.
Rundunar ta ce da misalin ƙarfe 10:00 na safe ta samu kiran gaggawa cewa gungun ‘yan bindiga masu yawa, a kan babura kusan 40, sun nufi makarantar da nufin sace ɗalibai da malamai.
Sai dai ‘yan sandan sun bayyana cewa babu tabbacin an yi nasarar sace ɗaliban makarantar yayin harin.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an tsaro sun ƙaddamar da bincike tare da bin sawun maharan cikin daji domin kama su. Ta ce an kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wani jami’in tsaro ya samu rauni a musayar wuta.
Sai dai wata kafar watsa labarai a jihar ta ruwaito cewa wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa an sace ɗalibai uku da wasu mutanen garin, lamarin da ke ci gaba da haifar da rudani kan adadin waɗanda abin ya shafa.