Ƙasar Pakistan ta kai hare-haren sama a yankin iyakarta da Afghanistan, lamarin da ya tayar da sabon rikici tare da kawo ƙarshen watanni na kwanciyar hankali a wannan yanki mai fama da rashin tsaro.

Ministan yaɗa labaran Pakistan, Attaullah Tarar, ya ce a ranar Laraba an lalata wurare huɗu a wani farmaki na sojin sama da aka shirya cikin tsari, inda aka kashe ‘yan bindiga 26.

Sai dai gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta bayar da rahoton cewa hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 13, ciki har da yara 11.

A cewar Islamabad, Pakistan ta dade tana zargin Afghanistan da bai wa ‘yan ta’adda mafaka da ke kai hare-hare cikin ƙasar, zargin da gwamnatin Taliban ke ci gaba da musantawa.

Wannan sabon rikici shi ne na farko mai tsanani tun watan Fabrairu, lokacin da arangama a kan iyaka ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoban bara, bayan makonni na rikice-rikicen da suka yi muni a yankin.

Attaullah Tarar ya ce hare-haren sun kasance martani ne ga “sabbin hare-haren ta’addanci a Pakistan,” inda aka kai farmaki kan wuraren ɓuya da horar da ‘yan bindiga da kuma wuraren ajiye makamai a yankin iyaka.

Tun bayan rikicin da ya ɓarke a ƙarshen watan Fabrairu, ana ci gaba da samun ƙananan arangama lokaci-lokaci, yayin da ƙasashen duniya ke kira ga Islamabad da Kabul da su zauna teburin sulhu domin dawo da zaman lafiya.