Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran za ta fuskanci sakamako kan abin da ya kira jan ƙafa wajen tattaunawar neman sulhu.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Truth Social, Trump ya zargi Iran da jinkirta cimma yarjejeniya duk da cewa, a cewarsa, yarjejeniyar za ta kasance mai amfani ga ƙasar.
Trump ya ce, “Iran ta ɗauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa kan yarjejeniya da za ta amfane ta, yanzu kuma za ta fuskanci sakamakon hakan.”
Kalaman na Trump sun zo ne yayin da ake fuskantar sabon tashin hankali tsakanin Amurka da Iran, bayan rahotannin musayar hare-hare tsakanin ɓangarorin biyu sakamakon harbo wani jirgin sojin Amurka da Iran ta yi a kusa da mashigar Hormuz.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran a matsayin martani, yayin da Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai kan sansanonin Amurka da ke wasu ƙasashen yankin.