Tawagar manyan jami’ai daga ƙasar Qatar ta isa birnin Tehran domin ganawa da jami’an gwamnatin Iran, a wani yunkuri na tattaunawa kan dangantakar ƙasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na Iran sun ce bangarorin za su yi musayar ra’ayoyi kan huldar da ke tsakaninsu, tare da duba sabbin ci gaban da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.

Jaridar gwamnatin Iran ta ce tattaunawar za ta kuma mayar da hankali kan ƙoƙarin diflomasiyya na warware rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka, baya ga sauran batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiyar yankin.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sabon tashin hankali tsakanin Tehran da Washington, bayan rahotannin musayar hare-hare tsakanin bangarorin biyu da kuma ikirarin Iran na harbo wani jirgin yaƙin Amurka.

Haka kuma, shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Iran za ta fuskanci sakamakon abin da ya kira jan kafa wajen tattaunawar zaman lafiya.

A nata bangaren, Iran ta shaida cewa za ta sake nazarin matakanta kan ci gaba da tattaunawar bayan hare-haren baya-bayan nan da Amurka ta kaddamar.