Majalisar Dattawa ta tsallake karatu na biyu ga wasu ƙudurorin dokar da ke neman ƙara yawan alƙalan manyan kotunan ƙasar domin rage cunkoso a harkar shari’a da kuma hanzarta yanke hukunci.

Ƙudurorin sun tanadi ƙara yawan alƙalan Babbar Kotun Tarayya daga 70 zuwa 90, yayin da za a ƙara yawan alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara daga 70 zuwa 110.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, wanda ya gabatar da ƙudurorin, ya ce matakin zai ƙara wa ɓangaren shari’a ƙarfi wajen tafiyar da yawan shari’o’in da ke ƙaruwa a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ba za ta bunƙasa yadda ya kamata ba idan ba a samu hukunci cikin gaggawa ba, yana mai jaddada buƙatar samar da isassun ma’aikata da kayan aiki ga ɓangaren shari’a.

Haka kuma, ƙudurorin sun tanadi tabbatar da daidaiton wakilcin jihohi da kuma Federal Capital Territory a Kotun Ɗaukaka Ƙara, tare da inganta tsarin gudanarwa da ayyukan kotun