Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na rage talauci ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na jihohin Arewa maso Yamma kan hanyoyin rage talauci, wanda UNICEF da Tarayyar Turai suka shirya.
Ya ce talauci na ci gaba da zama babban ƙalubale a yankin, inda yake shafar miliyoyin mutane ta fannin ilimi, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki da damar samun abin yi. Ya ƙara da cewa magance matsalar na buƙatar haɗin kai da jajircewar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya kuma yaba wa UNICEF da Tarayyar Turai bisa tallafin da suke bayarwa, tare da jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da haɗa kai da abokan hulɗa domin rage talauci da bunƙasa rayuwar al’umma.