Rundunar Nigeria Police Force a jihar Kano ta kama wata mata mai suna Maryam Usman, mai shekaru 32, bisa zargin banka wa ɗakin kishiyarta wuta a unguwar Mangwarori da ke Mariri, lamarin da ya jikkata mutum huɗu.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar 13 ga Mayu, 2026, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:40 na dare a ranar 12 ga Mayu, bayan samun rahoton gaggawa cewa wacce ake zargi ta banka wa ɗakin kishiyarta, Firdausi Saminu mai shekaru 40, wuta.

Wadanda suka jikkata sun haɗa da Firdausi Saminu, da yara biyu — Isma’il Saminu mai shekaru uku da Khadija Saminu mai shekaru biyar — tare da mijin, Saminu Miko.

Sanarwar ta ce an garzaya da su zuwa Asibitin Kwararru na Sir Sunusi da ke Kano domin samun kulawa.

Rundunar ta bayyana cewa jami’an sintiri sun kai ɗauki cikin gaggawa kuma sun kama wacce ake zargi a wurin da abin ya faru, inda yanzu haka take tsare a ofishin ’yan sanda na Mariri.

Bincike na ci gaba, kuma za a miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar da ke Bompai domin kammala bincike kafin gurfanar da ita a kotu bisa tuhume-tuhumen ƙona gida da yunƙurin kisan kai.


CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ANIPR, MNISMA, FNACSP,

Police Public Relations Officer

For: Commissioner of Police

Kano State Command.