Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen inganta wasu sassan tattalin arzikin Najeriya, amma ya nuna damuwa cewa fiye da kashi 63 cikin 100 na ’yan ƙasar har yanzu na rayuwa cikin talauci.


A rahotonsa na shekara-shekara kan tattalin arzikin Najeriya, IMF ya ce duk da ci gaban da aka samu a wasu fannoni, miliyoyin ’yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa.


Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur tare da aiwatar da sauye-sauye a tsarin canjin kuɗaɗen waje da haraji.


Masana tattalin arziki sun ce waɗannan matakan sun zama dole, amma duk da haka talauci ya ci gaba da ƙaruwa, inda ya shafi kusan kashi 63 cikin 100 na al’ummar Najeriya zuwa ƙarshen shekarar 2025.


Rahoton ya kuma nuna cewa sama da mutum miliyan 27 sun fuskanci matsalar ƙarancin abinci a Najeriya a shekarar 2025.