Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma ta gudanar da wani taron tattaunawa na musamman a Kano domin samar da hanyoyin rage talauci ta hanyar fadada shirye-shiryen tallafin jin kai da samar da sabbin hanyoyin samun kudade.
A wajen taron, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, ya ce dole ne a dauki tsarin tallafin gudanar da rayuwa a matsayin jari na bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma, ba kawai tallafi ba.
Darakta Janar ta Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, Maryam Yahaya, ta bayyana cewa yankin na fuskantar matsaloli da suka hada da talauci, rashin tsaro, karancin ilimi da yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ke bukatar hadin gwiwar jihohin yankin.
Ita ma mataimakiyar wakiliyar UNICEF a Najeriya, Dr Rownak Khan, ta yi gargadin cewa yara a yankin na fuskantar kalubale kamar rashin abinci mai gina jiki da karancin samun muhimman ayyukan kiwon lafiya da ilimi.
Mahalarta taron sun bayyana fatan cewa karfafa hadin gwiwar jihohi da fadada shirye-shiryen kariyar zamantakewa za su taimaka wajen rage talauci da inganta rayuwar al’ummar Arewa maso Yamma.