Rundunar 'Yansandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane 345 da ake zargi da hannu a ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai masu haɗari a wani samame na musamman da ta gudanar a faɗin jihar cikin kwanaki uku.

Da yake jawabi ga manema labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Bompai a ranar Litinin, Kwamishinan 'Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne bisa umarnin Babban Sufeton 'Yansandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, tare da amfani da sahihan bayanan sirri da kuma rahotannin da aka samu daga al'umma.

A cewarsa, samamen ya gudana ne tsakanin ranar 5 zuwa 7 ga watan Yunin 2026 a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda jami'an tsaro suka mayar da hankali kan wuraren da ake yawan aikata laifuka, maɓoyar 'yan daba da kuma wuraren da ake ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

CP Bakori ya bayyana cewa daga cikin nasarorin da aka samu akwai kama mutane 345 da ake zargi da laifuka daban-daban, waɗanda ake ci gaba da bincike a kansu kafin gurfanar da su a gaban kotu.

Ya ce rundunar ta kuma ƙwato makamai masu haɗari guda 270, ciki har da wuƙaƙe, adduna, gatari da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen tayar da tarzoma da aikata laifuka.

Haka kuma, jami'an tsaron sun kwato miyagun ƙwayoyi iri daban-daban da suka haɗa da tabar wiwi, ƙwayoyin Exol, Pregabalin, madarar sukudaye da aka fi sani da "Suck and Die", da sauran nau'o'in kayan maye.

Kwamishinan ya ce wannan aiki ya taimaka wajen daƙile ayyukan daba, rage ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma hana wasu manyan laifuka kamar fashi da makami, ƙwacen waya da sauran ayyukan ta'addanci.

Ya danganta nasarar da aka samu da ayyukan Operation Kukan Kura, wanda ke ƙara yawan sintirin jami'an tsaro a faɗin jihar, da kuma sabon Sashen Yaƙi da Manyan Laifuka (VCRU), wanda ya ƙara wa rundunar ƙarfin tattara bayanan sirri da saurin kai ɗauki.

CP Bakori ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi sassauci ga masu aikata laifuka ba, yana mai gargadin cewa duk wanda ya ci gaba da shiga harkokin daba ko ta'ammali da miyagun ƙwayoyi zai fuskanci hukuncin doka.

Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar da al'ummar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa jami'an tsaro, tare da kira ga jama'a da su ci gaba da bayar da bayanan sirri domin ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

A ƙarshe, Kwamishinan ya yi gargaɗi ga masu aikata laifuka da su daina ayyukansu ko kuma su fuskanci hukunci, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da samame da ayyukan tsaro ba tare da gajiyawa ba domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.