Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ta aiwatar sun taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, amma kuma sun zo da ƙalubale masu tsanani ga rayuwar al'umma, inda sama da 'yan Najeriya miliyan 60 suka ƙara faɗawa cikin talauci.

A cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, IMF ta ce matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka cikin shekaru uku da suka gabata, ciki har da cire tallafin man fetur, sauya tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje da kuma gyaran tsarin haraji, sun taimaka wajen daidaita wasu fannoni na tattalin arzikin ƙasar.

Sai dai duk da yabon da masana tattalin arziki ke yi wa waɗannan sauye-sauye, rahoton ya nuna cewa kusan kashi 63 cikin 100 na 'yan Najeriya na rayuwa cikin talauci, yayin da mutum miliyan 27 ke fuskantar matsananciyar barazanar rashin wadataccen abinci.

IMF ta bayyana cewa matsalar talauci ta daɗe tana addabar Najeriya, inda wani rahoton World Bank ya nuna cewa kusan kashi 69 cikin 100 na al'ummar ƙasar na fama da talauci, idan aka kwatanta da kashi 40 cikin 100 da aka samu a shekarar 2019.

Rahoton ya kuma nuna cewa kusan kashi uku cikin huɗu na mutanen da suka faɗa cikin talauci sun shiga wannan hali ne kafin shekarar 2023, lokacin da aka rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.

IMF ta yi gargadin cewa matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar yankunan arewacin Najeriya, inda ake samar da mafi yawan kayan abinci, na iya ci gaba da yin barazana ga ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

Hukumar ta kuma yi nuni da cewa hauhawar farashin kayan abinci, takin zamani da man fetur na iya ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga gwamnati, amma a lokaci guda su ƙara jefa talakawa cikin matsin rayuwa, lamarin da zai iya ƙara yawan mutanen da ke fama da talauci da ƙarancin abinci.