Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana nazarin matakan da za ta ɗauka kan abin da ta kira hare-hare da cin zarafin da ake yi wa 'yan ƙasarta a Afrika ta Kudu, yayin da take shirin fara kwashe wasu daga cikinsu daga ƙasar a ranar Laraba.

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Ojukwu, ta ce gwamnati na duba yiwuwar mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa, tare da ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya kan matakin da ya dace a ɗauka.

Ta zargi hukumomin South Africa da rashin ɗaukar matakan da suka dace domin dakile hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya, duk da cewa yawancin waɗanda ke zaune a ƙasar suna da takardun zama da aiki na halal kuma sun cika ƙa'idojin da doka ta tanada.

A cewarta, gwamnatin Najeriya ta samu rahotannin wawushe shagunan 'yan Najeriya, ƙona wasu daga cikinsu da kuma cin zarafin iyalansu, har ma da hana wasu yara zuwa makaranta.

Bianca Ojukwu ta soki gwamnatin Afrika ta Kudu kan rashin yin bayani mai ƙarfi ko ɗaukar tsauraran matakai don dakatar da lamarin, tana mai cewa Najeriya ba ta ji daɗin yadda ake mu'amala da 'yan ƙasarta ba.

Ministar ta kuma tunatar da irin gudunmawar da Najeriya ta bayar a lokacin gwagwarmayar kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata a Afrika ta Kudu, tana mai cewa hakan ya kamata ya ƙara ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun zanga-zangar adawa da baƙi a sassa daban-daban na Afrika ta Kudu, inda wasu masu zanga-zangar ke neman baƙin haure da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba su fice kafin ranar 30 ga watan Yuni.

A nasa ɓangaren, Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya sanar da wasu matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin daƙile kwararar baƙin haure, amma ya gargaɗi 'yan ƙasar da su guji ɗaukar doka a hannunsu.