Kasar Isra’ila ta ce tana ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Najeriya a bangaren noma, inda manoman Najeriya ke amfana da iri da sabbin fasahohin noma na Isra’ila.


A cewar jaridar Punch, Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya bayyana cewa kasarsa ta tallafa wa Najeriya da motocin daukar marasa lafiya domin inganta ayyukan kiwon lafiya.