Mataimakin Shugaban Ƙasar Amurka, JD Vance, ya ce Amurka da Israel suna da muradu iri ɗaya a fannoni da dama, sai dai akwai lokutan da manufofinsu kan bambanta.
Da yake magana da tashar Fox News a ranar Litinin, Vance ya bayyana cewa manufofin Washington kan Iran za su ci gaba da bin abin da shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ke ganin ya fi dacewa da muradun ƙasar.
“Muna da muradu iri ɗaya da Isra’ila, amma akwai lokuta da muradunmu ke bambanta,” in ji Vance.
Ya bayyana cewa babban burin Amurka shi ne tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.
A cewarsa, gwamnatin Amurka ta samar da yanayin da zai iya kaiwa ga cimma matsaya mai ɗorewa kan shirin nukiliyar Iran.
Sai dai ya ce irin wannan matsaya na iya zama abin da Isra’ila za ta amince da shi ko kuma ba za ta gamsu da shi ba, amma Amurka za ta ci gaba da bin abin da take ganin ya fi amfani ga ƙasarta.
“Isra’ila za ta iya amincewa da hakan ko kuma ba za ta amince ba, amma a ƙarshe muna ganin wannan shi ne mafi alheri ga Amurka,” in ji shi.
Vance ya jaddada cewa gwamnatin Amurka za ta ci gaba da ƙoƙarin cimma wannan buri, yana mai cewa shugaban ƙasa ne aka zaɓa domin aiwatar da manufofin da suka dace da muradun ƙasar.