Seyi Makinde ya bayyana cewa tasirin gwamnatin tarayya ba zai iya sauya sakamakon zaɓen 2027 ba, yana mai cewa ‘yan Najeriya za su fito su zaɓi shugabannin da suke so ba tare da tsoron tasirin siyasa ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron bunƙasa yawon buɗe ido na jihar Oyo da aka gudanar a cibiyar taruka ta Jami’ar Ibadan, inda ya ce jama’a ba za su ci gaba da zama masu kallo kawai ba a harkokin siyasa.

Ya kuma ce gwamnatinsa ta kafa tsare-tsare masu dorewa da za su tabbatar da ci gaban jihar bayan kammala wa’adinsa, yana mai cewa ko da yake zai iya ba da shawara kan wanda zai gaje shi, amma al’ummar Oyo ne za su yanke hukunci kan wanda zai zama gwamna na gaba.

Makinde ya gargadi jama’a da su guji zaɓen shugabanni marasa ƙwarewa, yana mai cewa kuskuren zaɓin shugaba na iya jefa jihar cikin matsala na tsawon shekaru huɗu.

Dangane da rade-radin goyon bayansa ga tsohon kwamishinan kuɗi, Bimbo Adekanbi, ya ce zai mara wa duk ɗan takara mai kishin jihar Oyo da ƙwarewar shugabanci baya, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba