Isra’ila ta sanar da sake rufe wuraren shiga da fita na Zirin Gaza bayan hare-haren da Iran ta kai a wasu sassan ƙasar, a wani mataki da mahukunta suka ce na da nasaba da tsaurara matakan tsaro.
Matakin ya shafi rufe mashigar Rafah da ta Kerem Shalom, waɗanda ke daga cikin manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen shigar da kayan agajin jin ƙai da sauran kayayyaki zuwa Zirin Gaza.
Hukumar Cogat, mai kula da ayyukan gwamnatin Isra’ila a yankunan Falasdinawa kuma ƙarƙashin Ma’aikatar Tsaron ƙasar, ta ce an ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na matakan tsaro da suka zama wajibi sakamakon halin da ake ciki.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta yi ikirarin cewa rufe mashigun ba zai haifar da wata matsala ta jin ƙai a Gaza ba, tana mai cewa kayan abinci da aka shigar da su yankin tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta sun zarce buƙatun al’ummar yankin.
Wannan ba shi ne karo na farko da Isra’ila ke rufe mashigun Gaza ba, domin ta taɓa ɗaukar irin wannan mataki a lokutan da rikici ya ƙara tsananta tsakaninta da Iran.
Matakin na zuwa ne yayin da ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji ke ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar ƙaruwar matsalolin jin ƙai a Gaza sakamakon rikice-rikicen da ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.