Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar da za su fafata a zaɓukan cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga Yunin 2026 a wasu kujerun Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisun Dokokin Jihohi.
A zaɓen Sanatan Ondo ta Kudu, ƴan takara huɗu ne za su fafata, waɗanda suka haɗa da Adesanya Olaoluwa na APP, Faduyile Francis Adedayo na APC, Akinwumi Adeolu Harrison na APM da kuma Nejo Funso Clement na BP.
A mazaɓar Sanatan Nasarawa ta Arewa kuwa, Halilu Danladi Envwulu-Aza ne zai yi takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da Maku Labaran ke wakiltar LP, John Paul Araneshri na NNPP da Emmanuel David Ombugadu na PDP.
A Jihar Rivers, kujerar Sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas za ta samu fafatawa tsakanin Douglas Fabeeke Beeka na AA, Osarosaka Ebenezer Erewari na APC, Sam Kinanee Barikpoa na LP da Nwogu Olaka Johnson na PDP.
Haka kuma, a Enugu ta Arewa, Asogwa Ikeje Israel na APC, Aneke Kingsley Chukwuebuka na BP da Ezeme Nestor Chika na PDP ne za su nemi kujerar.
Jerin sunayen ya kuma nuna cewa a mazaɓar Zuru ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Garba Aiki Rabiu na APC da Aliyu Galadima Muhammad na LP ne za su fafata.
A mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano kuwa, Rabiu Shuaibu na APC zai kara da Lawan Garba Haruna na APM da kuma Abubakar Yahaya Muhammad na LP.
Ana sa ran gudanar da waɗannan zaɓukan cike gurbi ne domin maye gurbin kujerun da suka zama babu wakilai sakamakon dalilai daban-daban.
INEC ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da ƴan takara da su bi ƙa’idojin yaƙin neman zaɓe tare da gudanar da harkokinsu cikin lumana domin tabbatar da sahihin zaɓe a ranar kaɗa ƙuri’a.