Jam’iyyar NDC ta sanar da ɗaukar wasu muhimman matakai da nufin ƙarfafa dimokuraɗiyya, ladabtarwa da haɗin kai a cikin jam’iyyar, yayin da take shirin tunkarar zaɓuɓɓuka masu zuwa.

An cimma matsayar ne a taro na biyu na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar, kamar yadda ke ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Osa Director, ya fitar a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, jam’iyyar ta amince da kafa kwamitin sulhu domin magance duk wata rashin jituwa da ka iya tasowa a tsakanin mambobinta tare da ƙarfafa haɗin kai a cikin gida.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa dukkan gwamnatocin da aka zaɓa ƙarƙashin tutarta za su riƙa tuntubar jam’iyyar kafin yanke manyan shawarwari da suka shafi manufofi, naɗa muƙamai da aiwatar da muhimman shirye-shirye.

Sai dai ta bayyana cewa wannan tsarin ba zai shafi naɗin ma’aikatan ofisoshin masu riƙe da muƙaman siyasa ba.

NDC ta jaddada cewa muradun jam’iyya sun fi muhimmanci fiye da na kowane mutum, tare da kira ga mambobinta da su daidaita manufofinsu da ayyukansu da akida da manufofin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce matakan da ta ɗauka za su taimaka wajen gina ƙaƙƙarfan tsari na shugabanci, ƙarfafa haɗin kai da kuma shirya jam’iyyar yadda ya kamata domin tunkarar zaɓuɓɓukan da ke tafe.