Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da dattijan wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara bayan sun amsa gayyatar yin sulhu da su domin kawo ƙarshen hare-haren da suka addabi yankin.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Magamin Diddi, wanda ke kusa da wani daji da ake zargin 'yan bindigar ke amfani da shi a matsayin mafaka.

Da yake zantawa da BBC, Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Sunusi Ahmed Dosara, ya ce tun watanni uku da suka gabata mazauna ƙauyen ke fama da hare-haren 'yan bindiga da suka hana su gudanar da harkokinsu cikin walwala.

Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun aika saƙon gayyatar dattawan ƙauyen zuwa tattaunawar sulhu, tare da alƙawarin barin al'ummar yankin su ci gaba da zirga-zirga da kasuwanci ba tare da tsangwama ba.

Sai dai bayan dattawan sun isa wurin ganawar a cikin daji, 'yan bindigar suka tsare su. Daga bisani sun saki wasu daga cikinsu tare da bayyana cewa ba za su sako sauran ba sai an biya wasu sharuɗɗa da suka gindaya.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce mutum 39 ne ke hannun masu garkuwar, kuma dukkansu maza ne manya da dattawa.

Ya ƙara da cewa yankin ya daɗe yana fama da matsalar 'yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba.

A cewarsa, dajin Bayan Ruwa, wanda ke yankin, na daga cikin manyan maboyar 'yan bindiga, inda suke fitowa suna tare matafiya a hanyoyin Zamfara zuwa Sokoto da Koko tare da yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da suka fi fama da matsalar 'yan bindiga, lamarin da ya janyo asarar rayuka, tarwatsa al'ummomi da kuma durƙusar da harkokin noma da kasuwanci, waɗanda su ne ginshiƙan tattalin arzikin yankin.