Manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya masu kula da harkokin ’yancin addini sun fara wata ziyarar aiki ta makwanni biyu a Najeriya domin nazarin halin da ake ciki game da ’yancin addini da zamantakewar al’umma a ƙasar.
Ziyarar na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da suka taso a shekarar da ta gabata kan zarge-zargen tauye ’yancin addini, musamman bayan wasu rahotanni da suka yi ikirarin cewa ana fuskantar ƙalubale wajen kare haƙƙin mabiya addinai daban-daban a Najeriya.
Masana da masu bincike kan harkokin tsaro sun ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta sun fi alaƙa da matsalar ta’addanci da hare-haren masu ikirarin jihadi a arewacin ƙasar, inda galibin waɗanda rikice-rikicen ke shafa Musulmi ne da Kiristoci baki ɗaya.
A lokacin ziyarar, Mai Ba da Rahoto ta Musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ’Yancin Addini ko Akida, Nazila Ghanea, za ta ziyarci Abuja da Kano da kuma Jos domin ganawa da jami’an gwamnati, shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Ghanea ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce fahimtar yanayin da ake ciki tare da gano hanyoyin da za su taimaka wajen ƙarfafa kare ’yancin addini da zaman lafiya tsakanin al’ummomin ƙasar.
Najeriya, mai yawan al’umma kusan miliyan 230, na da mabiyan addinai daban-daban da ke zaune a sassa daban-daban na ƙasar. Duk da kasancewar mafi yawan lokuta al’ummomin na rayuwa cikin zaman lafiya, ƙasar ta sha fama da rikice-rikicen da suka haɗa da na addini, kabilanci da kuma rikicin makiyaya da manoma.
Jihar Filato na daga cikin yankunan da suka fuskanci rikice-rikice a lokuta daban-daban, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta zarge-zargen cewa tana nuna wariya ko muzgunawa wata ƙungiyar addini, tana mai cewa matakan tsaro da ake ɗauka sun shafi yaƙi da masu tayar da kayar baya da sauran masu aikata laifuka ba tare da la’akari da addininsu ba.
Wasu masana kuma na ganin cewa yawancin rikice-rikicen da ake dangantawa da addini a Najeriya suna da alaƙa da matsalolin ƙasa, albarkatu, makiyaya da manoma, fiye da bambancin addini kai tsaye.