Hakan yabiyo bayan da jam’iyyar NDC ta cire wasu daga cikin ’yan takarar da tsagin Kwankwasiyya ya gabatar a Kano, tana mai cewa an karya yarjejeniyar da aka yi kan rabon mukamai da tikitin takara.


Shugaban NDC na Kano, Hussaini Isah Mairiga, ya bayyana cewa an yi sauyin ne domin a bi yarjejeniyar da aka cimma tsakanin jam’iyyar da Kwankwasiyya.


A cewar jam’iyyar, an amince cewa Kwankwasiyya za ta samu kashi 60% na mukamai da tikitin takara, yayin da tsofaffin ’yan jam’iyyar za su samu kashi 40%.


Sauye-sauyen sun shafi wasu ’yan takarar Majalisar Wakilai da kuma na Majalisar Dokokin Jihar Kano a wasu mazabu.

Shin meza kuce?