Iran ta zargi Amurka da hana wasu manyan jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar, duk da amincewa da bai wa ‘yan wasa da wasu ma’aikatan tawagar bizar halartar Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Mahukuntan Iran sun ce an ƙi bai wa wasu jami’an gudanarwa da masu ba da shawara biza, lamarin da suka bayyana a matsayin katsalandan a harkokin wasanni saboda dalilai na siyasa.

Sai dai gwamnatin Amurka ta ce ta bayar da biza ga ‘yan wasa da sauran ma’aikatan da ake buƙata domin halartar gasar, tana mai jaddada cewa ba za ta amince a yi amfani da tsarin gasar wajen shigar da mutanen da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin da ta ke kallon barazana ga tsaro ba.

Iran ta kuma yi kira ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) da ta shiga cikin lamarin, yayin da rahotanni daga ƙasar suka nuna cewa shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Iran da mataimakinsa na cikin waɗanda aka hana shiga Amurka.

A makon nan, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa ba za a bai wa mutanen da ke da alaƙa da Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) damar shiga cikin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar ba.

Ana sa ran Iran za ta fara fafatawa a gasar Kofin Duniya ta 2026 a ranar 15 ga Yuni, inda za ta buga wasanta na farko a birnin Los Angeles. Gasar za ta gudana ne a ƙasashen United States, Canada da Mexico.