Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta yi barazanar rufe Mashigar Hormuz gaba ɗaya ga zirga-zirgar jiragen da ke jigilar mai da iskar gas, yayin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari a yankin Tekun Fasha.

Hukumar ta ce za ta iya ɗaukar wannan mataki a matsayin martani idan Amurka ta ci gaba da abin da ta bayyana a matsayin ayyukan tsokana da kuma cin zarafin ikon ƙasar Iran.

Barazanar ta zo ne bayan Amurka ta sanar da cewa dakarunta sun kai hare-hare kan wasu na’urorin sa ido da ke yankunan gaɓar teku na Goruk da Qeshm a Iran.

A nata ɓangaren, rundunar IRGC ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa wasu sansanonin sojojin Amurka da ke ƙasashen Bahrain da Kuwait.

Sai dai rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, ta ce an yi nasarar kakkabo makaman ko kuma sun kasa kaiwa wuraren da aka nufa.

Lamarin ya ƙara haifar da fargaba a kasuwannin makamashi na duniya, kasancewar Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin da ake bi wajen jigilar ɗimbin man fetur da iskar gas zuwa sassa daban-daban na duniya.

Masana na gargadin cewa duk wani cikas ga zirga-zirga a mashigar na iya haifar da tashin farashin makamashi tare da kawo tangarɗa ga kasuwannin duniya.