Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga 700,000 a rana, bayan wani gwajin da hukumomin da ke kula da harkokin matatun mai suka gudanar.

Sabon adadin ya nuna cewa matatar ta ƙara ƙarfin aikinta daga ganga 650,000 zuwa 700,000 a kowace rana, lamarin da ke ƙara kusantar da ita ga burinta na zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya.

Mataimakin shugaban sashen mai da iskar gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce wannan ci gaban na cikin shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan matatar domin ninka yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin shekaru biyu da rabi masu zuwa.

Tun bayan fara aiki, matatar Dangote ta samu karɓuwa a kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje, inda take taka muhimmiyar rawa wajen samar da man jiragen sama da sauran kayayyakin man fetur ga ƙasashe daban-daban.

Sai dai duk da nasarorin da take samu, matatar na ci gaba da fuskantar wasu ƙalubale a Najeriya. Daga cikin matsalolin akwai rashin gamsuwa da wasu manufofin gwamnati, musamman batun bai wa wasu kamfanoni damar shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.