Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bukaci dukkan alhazan kasar da ke shirin komawa gida bayan kammala aikin Hajjin bana da su tabbatar sun cike takardar bayanan lafiyarsu (Health Declaration Form) kafin tashinsu daga Saudiyya.
Kamar yadda wata sanarwa ta bayyana, tuni aka raba takardar ga tawagogin likitocin jihohi tun daga tashin jirgin farko na alhazan bana. Hukumar ta ce ana bukatar tawagogin likitocin jihohi su taimaka wa alhazan da ba su iya karatu ko rubutu wajen cike takardar domin kauce wa jinkirin da ka iya tasowa a filayen jiragen sama da zarar sun isa Najeriya.
Sanarwar ta ce an samu irin wannan jinkiri a filin jirgin saman Legas a ranar da ta gabata sakamakon rashin kammala cike wasu daga cikin takardun bayanan lafiyar da ake bukata.
Hukumar ta kuma bukaci alhazan da suka iya amfani da na’urorin zamani da su cike takardar ta yanar gizo kafin ranar tashinsu, yayin da aka umarci tawagogin likitocin jihohi da su ba da dukkan goyon bayan da ake bukata domin tabbatar da cewa kowane mahajjaci ya cika wannan sharadi kafin komawa gida.