Wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun yi garkuwa da ɗalibai shida na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Ƙauran-Namoda a jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da ɗaliban ke zaune a wajen harabar makarantar.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani gida da ke gefen unguwar Low-Cost a garin Ƙauran-Namoda, inda maharan suka kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da daliban.
Shugaban ƙaramar hukumar, Mannir Haidara Ƙaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.
“Lamarin ya faru; kuma jami’an tsaro suna cigaba da gudanar da aiki domin ceto ɗaliban da aka sace, tare da mayar da su ga iyalansu lafiya”, in ji shi.
Wani ɗalibi a makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa dasu ya samu damar kuɓuta daga hannun maharan, lamarin da ya rage adadin waɗanda ke tsare zuwa shida, waɗanda suka haɗa da maza uku da mata uku.
Ita ma Rundunar Ƴansandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya ce jami’an rundunar tare da dakarun ‘Operation Fansan Yamma’ sun fara wani samame na musamman domin ceto ɗaliban.