Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane tare da kwato makamai a Karamar Hukumar Baruten, Jami’ar Yaɗa Labaran Rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ne ya fitar da sanarwar


Sanarwar ta ce ’yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi yayin wani samame da suka kai a yankin Tabida da ke Okuta, kafin daga bisani bincike ya kai ga gano Umar Abubakar wanda aka fi sani da Manti a matsayin wanda ake zargin yana jagorantar masu garkuwa da mutane a wasu yankuna.


Rundunar ta ce bincike ya nuna wanda ake zargin na da hannu a hare-haren garkuwa da mutane a wasu sassan Kwara ta Arewa, musamman a yankunan Okuta, Ilesha Baruba da Tabida, yayin da aka kwato makamai biyu daga hannun wadanda ake zargin.


Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ake zargi da hannu a laifukan, tare da gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.