Ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi barazanar bayyana sunayen ‘yan siyasar da ke da hannu a sace ɗalibai a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.


Igboho ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da sabbin shugabannin ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa (NANS) ƙarƙashin jagorancin Akinteye Bàbàtunde a gidansa da ke yankin Soka a Ibadan ranar Laraba.


A cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, wanda Wisdom TV ta ɗauka, Igboho ya ce ya bayar da kansa domin korar ‘yan bindigar da suka aikata satar, amma gwamnatin jihar ta nuna rashin amincewa da hakan.


Ya kuma yi iƙirarin cewa bai taɓa neman ko sisin kwabo daga gwamnatin Jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde domin ceto mutum 47 da aka sace ba.