Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wakilan kungiyar sama da 132 a Kano, inda ya ce gudummawar da suke bayarwa ta taka muhimmiyar rawa wajen yada ayyuka, nasarori da manufofin tafiyar Kwankwasiyya a kafafen zamani.


A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar, Gwarzo ya ce yana matukar girmama mambobin kungiyar saboda jajircewarsu da kwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu.


Ya ce, “Muna da matukar girmamawa ga kungiyar masu yada manufofin Kwankwasiyya a kafafen sada zumunta, kuma suna sanya mu alfahari.”


Dan takarar ya kuma bayyana cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna jin dadinsa da irin kokarin da kungiyar ke yi.


“Jagoranmu na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana farin ciki da ku kuma yana alfahari da irin rawar da kuke takawa,” in ji shi.


Gwarzo ya yi alkawarin ba kungiyar fifiko wajen horaswa da bunkasa kwarewa, yana mai jaddada muhimmancin koyon sabbin dabaru da fasahohi a duniyar sadarwa ta zamani.


Ya ce za su samar da damammakin horaswa tare da kayan aiki da dabarun zamani da za su taimaka wajen kara inganta ayyukan mambobin kungiyar.


Haka kuma ya tabbatar musu da cikakken goyon baya da hadin kai domin kara kusantar da tafiyar ga jama’a da fadada tasirinta.


A karshe, Gwarzo ya bukaci mambobin kungiyar da su ci gaba da kasancewa masu mayar da hankali kan aikinsu, tare da kiyaye kwarewa da da’a yayin yada sakonnin tafiyar a kafafen sada zumunta.